Al Maliki ya ce Iraqi za ta iya tafiyar da harkokin tsaronta

Nuri Maliki
Image caption Firayim Ministan Iraki, Nuri Al Maliki

A yayinda dakarun Amurka a Iraqi ke shirin tattara ya-nasu- ya -nasu su kaucewa fagen daga a hukumance, Pirayim Ministan Iraqin Nuri al-Maliki, ya bayyana wadanda ke ganin kasarsa ba za ta iya ci gaba da rayuwa, ba tare da dakarun Amurka ba da cewa makiyan kasar ne.

Mr al-Maliki ya tsaya kai da fata cewa dakarun Iraqi da yan-sandanta na iya tabbatar da tsaro, kuma ya ce Iraqi na ci gaba da murmurewa a kokarin sake samun yancin kanta.

A wani jawabi da yayi ga 'yan kasar ta talabiji, Nuri Al-maliki ya ce tun bayan da aka bada sanarwar janye sojojin Amurka daga kasar,kasar ta sa ta maido da 'yancinta.

Ya ce; "A yau, Iraki kasa ce mai 'yanci,kuma ita ce ke da nauyin dukkanin abubuwan da suka shafe ta.

Ranar talatin da daya ga watan Agusta zata kasance ranar da 'yan kasar ta Iraki ba zasu manta da ita ba domin kuwa zasu kasance masu alfahari.

"Daga yau,sojojinmu,da kuma sauran jami'an tsaro za su ci gaba da tabbatar da tsaron kasar,da kuma kare ta daga duk wani farmaki daga ciki ko wajen kasar." In ji Al Maliki

A Amurka kuma shugaba Obama na gana tare da dakarun kasar a sansanin soji na Texas domin bayyana godiyarsa game da aikin da suka yi a Iraqi.

Idan an jima ne ake sa ran zai yi jawabi a kafar talabijin inda ake tsammanin zai tabbatar da ci gaban huldar diflomasiyya da na siyasa tsakanin Amurkar da Iraqi.

Har yanzu dai akwai sojojin Amurka dubu 50 da za su ci gaba da zama a Iraki a matsayin masu bada shawara, kuma a Amirka ta amince ta janye su a karshen shekara mai zuwa.