Barnar ambaliyar ruwa a jihar Katsina

A Nijeriya wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa a jihar Katsina sun haddasa mutuwar akalla mutane bakwai da dabbobi da kuma hasarar dukiya mai dimbin yawa.

Ambaliyar ruwan, wadda ta shafi sassa daban-daban na jihar, ta share wani kauye baki-dayansa, yayinda a babban birnin jihar bangayen da suka yi ruma, saboda yawan ruwan saman, suka rika afka wa jama'a.

Matsalar ta ambaliyar ruwa dai ta shafi jihohi da dama a Arewacin Nijeriar da kuma kasashe makwabta irinsu Jumhuriyar Nijar da Chadi.