An kama jagoran dillalan kwayoyi a Mexico

Jagoran dillancin kwayoyi, Edgar Valdez
Image caption an kame Mista Valdez ne bayan shekara ana binsa sau da kafa

Hukumomi a kasar Mexico sun bayar da rahoton cewa an kame daya daga cikin dillalan miyagun kwayoyin da ake nema ruwa-a-jallo a kasar, wato Edgar Valdez.

An fi sanin Mista valdez ne da sunan ‘Barbie’, ko 'yar tsana, saboda kamanninsa: yana da farar fata da kuma shudayen idanduna.

A Texas ta kasar Amurka aka haife shi, yayin da karansa ya yi tsaiko a tsakanin kungiyoyin masu aikata miyagun laifuffuka na Mexico a shekaru goman da suka gabata.

Ya kuma kasance daya daga cikin manyan na hannun daman shugaban kungiyar masu fataucin miyagun kwayoyi ta Beltran Leyva, wadda take da karfi sosai a tsakiyar kasar ta Mexico.

Tun bayan kisan shugaban kungiyar a watan Disamban bara ne kuma ya ke ta hankoron zama jagoranta.

'Yan sanda a Mexico da ma Amurka sun dade suna neman Mista ruwa-a-jallo.

A cewar rahoton 'yansandan da ya tabbatar da kama shi, tun watan Yunin bara ne 'yansandan su ke binsa sau da kafa.

Shugaban Mexico, Felipe Calderon dai ya nuna farin cikinsa da kama Mista Valdez ta twitter da kuma shafinsa na intanet.