Rundunar yansandan Najeriya ta janye shingayen hanyoyi

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kawar da shingayen da jami'anta suka kakkafa don duba ababen hawa a kan manyan hanyoyin wasu sassan kasar.

Hakan ya biyo bayan koke-koken da ake ta yi ne a kan yadda ire-iren wadannan shingaye suka zama wuraren da ake zargin 'yan sanda suna karbar kudade daga hannun jama'a ba bisa ka'ida ba.

Wani rahoton kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch ya yi zargin 'yan sanda sun karbi fiye da Naira miliyan dubu ashirin a cikin shekara daya da rabi.

Ana kuma zargin 'yan sandan da cin zarafin matafiya, wani zubin ma har da halaka mai abin hawa idan ya bijirewa bayar da na goron a wadannan shingaye.