An sallami manyan jami'an tsaro a Kamaru

Hukumomi a jamhuriyar Kamaru sun bayyana daukar wasu matakan tsaurara tsaro, da kuma samun bayanai game ababuwan da ke faruwa a cikin kasar.

A sakamakon haka ne, Shugaban kasar Paul Biya ya nada wasu sababbin jami'an da za su kula da wadannan fannonin.

Hakan kuwa ya biyo bayan sauke masu rike da wadannan mukamai da Shugaban yayi tun farko.

Wannan shi ne karon farko da haka ta faru, tun bayan yunkurin juyin mulkin da ya ci tura a 1984.

Jama'a dai na kallon wannan ba ya rasa nasaba da sakacin tsaro da jami'an tsaron ke nunawa, ta hanyar karbar na goro don fallasa bayanan sirri na kasa.