An umurci sojojin Isra'ila su mayar da martani

Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Image caption Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ba jami'an tsaro umurnin mayar da martani

Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya umurci jami'an tsaro da su mayar da martani ba tare da wani tarnaki na diflomasiyya ba a kan kisan wadansu ’yan Isra'ila guda hudu da aka yi a daura da garin Hebron a gabar yammacin Kogin Jordan.

’Yan Israilan da abin ya shafa dai mata biyu ne, da maza biyu.

Da ya ke jawabi a lokacin da ya isa birnin Washington don farfado da tattaunawar sulhu a Gabas ta Tsakiya, Mista Netanyahu ya ce harbin mutanen ya karawa Israila kaimi a kudurinta na kin sassautawa kan abubuwan da suka shafi tsaronta.

Mayakan kungiyar Falasdinawa ta Hamas sun ce su ne suka kai harin.