An fara aiwatar da dokar sanya hular kwano a Nijar

Image caption Tutar jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar, jami'an 'yan sanda sun fara aiwatar da wata doka mai tilasta wa duk wani wanda zai hau babur ko moto amfani da hular kwano.

Matakin na daga cikin tsarin da hukumomin 'yan sandan suka yi a baya-bayan nan domin taimaka wa ga rage munin haduran da ke aukuwa barkatai a kasar musamman ma wajen masu babura.

A kwanakin baya ne dai ma'aikatar ministan cikin gida ta sa hannu a dokar, kuma duk wanda aka samu da laifi sai an ci shi tara.