Bama-bamai sun hallaka mutane 18 a Pakistan

Image caption Yankin da bam din ya tashi

Bama bamai uku sun tashi a birnin Lahore na kasar Pakistan, a lokacin wani jerin gwano da dubban yan Shia suka gudanar.

'Yan sanda sun ce akalla mutane 18 ne suka halaka kuma fiye da 100 suka jikkata sakamakon bama baman da suka tashi da kuma tirmitsitsinda hakan ya haifar.

Wakilin BBC ya ce dama akwai tarihi a kasar Pakistan na irin wannan hari inda masu tsattsauran raayin Sunni suke kai hare-hare a lokacin bukukuwan 'yan Shia da wuraren bautarsu, inda suke kallon 'yan Shiar a matsayin kafirai.