Janar Buhari ya sha ruwa da Shugaba Jonathan

Janar Muhammadu Buhari mai ritaya
Image caption Janar Muhammadu Buhari ya ziyarci Shugaba Goodluck Jonathan a fadarsa

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya ziyarci Shugaba Goodluck Jonathan a fadarsa, ko da yake babu karin bayani a kan takamaiman abin da suka tattauna.

Fadar Shugaban kasar dai ta ce ganawar Shugaba Goodluck Jonathan da tsofaffin shugabannin Najeriya ba sabon abu ba ne.

Shi dai Janar Muhammadu Buhari ya kauracewa fadar shugaban kasar tsawon shekaru amma kuma tun rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa ya koma ziyartar fadar.

To ko menene ya kai tsohon shugaban kasar gidan gwamnati?

Injiniya Buba Galadima, wani na hannun daman tsohon shugaban kasar ta Najeriya, kuma dan kwamitin amintattu na jam’iyyarsa ta CPC, ya shaidawa BBC cewa Janar Buhari ya amsa gayyatar da aka yi masa ne ta shan ruwa tare da Shugaba Jonathan.

“Ya isa wurin an yi bude-baki da shi; sun zauna na kusan awa biyu...kuma idan manya irin wadannan suka sadu dole su tattauna abin da zai [kawowa] kasar alheri, zai yiwa kasa kyau, zai kuma kawo ci gaban al’umma”, inji Injiniya Buba Galadima.

Sai dai dan kwamitintattun na jam’iyyar CPC ya wannan ziyara da Janar Buhari ya kaiwa Shugaba Goodluck Jonathan “ba [ta] canja mana alkibla ba, bai canja mana manufarmu ta kwato Najeriya daga hannun azzalumai ba, bai canja mana kuma alkibla na cewa lallai, lallai kasar nan a yi gaskiya a zauna a kan gaskiya, a tabbatar da gaskiya ba”.