Taro kan habaka noma a Afrika

Wasu manoma maata a Afrika
Image caption Kasashe da dama a Afrika na fama da karancin abinci

An fara wani taron yini uku a birnin Accra na Ghana kan yadda za a habaka harkokin noma da samarda abinci a kasashen Africa.

Masu halartan taron dai sun hada da tsohon Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan da tsohon shugaban Nigeria Cif Olusegun Obasanjo da Prime Ministan Tanzania, da kuma Mataimakin Shugaban kasar Ghana,John Mahama. Wata kungiya mai zaman kanta ta raya ayyukan noma ,mai suna AGRA a takaice, da gidauniyar Rockfeller Foundation tare da hadin gwiwar gwamnatin Ghana ne dai suka shirya taron, wanda wakilai sama da dari uku ke halarta.