Ana sace magungunan maleriya a Afirka

Sauro
Image caption Fiye da mutane miliyan daya ne ke rasuwa ta hanayr maleriya duk shekara a yankin Afirka kudu da hamada

Wani sabon bincike ya tabbatar da cewa ana sace magungunan zazzabin cizon sauro, ko maleriya, wadanda da ake ba kasashen Afirka a matsayin tallafi, ana kuma karkatar da su zuwa kasuwannin bayan fage.

Masu sharhi dai sun bayyana cewa sakamakon binciken, wanda aka wallafa a wata mujalla ta binciken magunguna a kasashe masu zafi, bai zo da mamaki ba, amma masu ba da agaji sun ki su ce komai a kan batun.

Wadanda suka gudanar da binciken dai sun sayi magungunan maleriya ne a kantunan magani masu zaman kansu tsakanin shekarar 2007 da kuma 2010 a birane goma sha daya na Afirka.

Sun kuma gano cewa kusan kashi shida da digo biyar cikin dari na magungunan kamata ya yi a kai su asibitocin gwamnatocin kasashen na Afirka don bayar das u kyauta ga marasa lafiya.

Maganin da aka fi sacewa dai shi ne samfurin Artemesinin, wanda shi ne maganin maleriya mafi karfi.

A shekarar 2007 kashi goma sha biyar cikin dari na magungunan da aka bayar da tallafinsu aka sace—adadin da ya karu zuwa kashi talatin cikin dari a shekarar 2010.

Mawallafa rahoton dai sun ce yawan samfurin da aka yi amfani da shi wajen gudanar da binciken ba shi da yawa; hakan kuma ka iya kambama al'amarin.

Sai dai masu bayar da agaji sun tabbatar da cewa magunguna kan bace kuma akwai kanshin gaskiya a cikin sakamakon binciken.

Wani bincike da Amurka ta gudanar bara dai ya gano cewa magungunan maleriya da kudinsu ya kai dala dubu dari shida da arba'in ne suka bace a filayen jiragen sama da dakunan ajiyar magunguna na kasar Angola.

Binciken ya kuma gano cewa akan yi safarar magungunan daga wata kasa zuwa wata.

Alal misali, an samu magungunan da aka aike da su don amfanin al’ummar Gabashin Afirka a shagunan ‘yan kasuwa a Yammacin Afirka.

Fiye da mutane miliyan daya ne dai ke rasa rayukansu a yankin afirka kudu da Sahara sakamakon zazzabin cizon sauro.