Masu fina finan Hausa a Najeriya na neman a binciki wani jami'i

Kano a taswirar Najeriya
Image caption Kano a taswirar Najeriya

Kungiyar masu shirya fina finan Hausa a Najeriya, MOPPAN, ta maida martani dangane da zargin da ake yi wa shugaban hukumar tace finafinai da dab'i ta jahar Kano, Malam Abubakar Rabo Abdulkarim, na yin lalata da wata karamar yarinya.

Duk da cewa gwamnatin jihar Kanon ta fito tana cewa zargin ba shi da tushe, kungiyar ta masu sana'ar fim din Hausa na cewa, ya kamata a gudanar da sahihin bincike, tana mai zargin gwamnatin Kanon da neman yin rufa rufa.

A yanzu 'yan kungiyar ta MOPPAN na kurarin dakatar da kai fina finansu hukumar da Malam Abubakar Rabo Abdulkarim ke jagoranta domin tacewa, har sai gwamnatin Kano ta gudanar da bincike kan batun.

Da ma dai an sha kai ruwa rana tsakanin masu shirya fina finan da shugaban hukumar tace fina finan, lamarin da ya kai su ga mayar da wasu ofisoshinsu jihar Kaduna.