INEC ta yanke shawara kan wa'adin wasu gwamnoni

Shugaban Hukumar INEC, Profesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar INEC ta ce sabuwar dokar na cikin sauyen sauyen da aka gudunar a dokokin zaben kasar

Hukumar zaben Nigeriya mai zaman kanta wato INEC ta ce shidda daga cikin gwamnonin jihohin kasar da aka sake gudanar da zaben su, za su kammala wa'adinsu a ranar 29 na watan Mayun shekara mai zuwa, tare da sauran gwamnoni.

Hukumar ta INEC ta ce sabuwar dokar na cikin sauyen sauyen da aka gudunar a dokokin zaben kasar .

Sai dai kuma hukumar ta ce dokar ba zata shafi wasu gwamnonin jihohi hudu da su ma aka sake zabe a jihohinsu ba, wadanda su sai nan gaba nasu wa'adin mulkin zai kare.

Sai dai kuma wasu masana harkokin shari'a , na cewa matakin ya saba ma dokokin kasa.