Gobara a dandamalin mai a gabar tekun Mexico

Dandamalin hakar mai
Image caption Dandamalin hakar mai

An aike da jiragen ruwan kashe gobara zuwa wani dandamalin hakar mai dake gabar tekun mexico na kasar Amurka, domin kashe gobarar da ta tashi, sakamakon fashewar wasu abubuwa.

Dandamalin na kamfanin Mariner Energy, har yanzu yana ci da wuta, kuma masu tsaron gaba sun ce burbushin mai ya bazu zuwa kusan mil daya daga dandamalin.

Wasu masu gadin gabar teku sun ce dukkan ma'aikata goma sha ukun dake aiki a dandamalin sun tsira.

Lamarin ya faru a wani yanki da ke yammacin wani dandamalin da ya tarwatse a farkon wannan shekara, inda aka sami malalar mai sosai.