Pakistan ta yi tur da hari kan 'yan shi'a

Firayim Minista Yousuf Raza Gilani na Pakistan
Image caption Yousuf Raza Gilani ya ce wadanda suka kai harin ba za su tserewa hukunci ba

Firayim Ministan Pakistan, Yousuf Gilani ya yi tur da hare-haren kunar bakin wake guda uku da aka kaiwa wani jerin gwanon ’yan Shi'a a birnin Lahore da ke gabashin kasar.

Akalla mutane talatin da daya ne aka kashe, sannan aka raunana wadansu dari biyu da hamsin a hare-haren.

Mista Gilani ya ce masu wasa da rayukan mutanen da ba su ji ba basu gani ba ba za su tserewa hukunci ba.

Bayan hare-haren dai masu muzaharar sun afkawa ’yan sanda wadanda suka zarga da gaza ba su kariya, abin da ya sa ’yan sandan amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsasu.

Karin bayani