Tattaunawar Isra'ila da Falasdinawa

Shugaba Obama na Amurka tare da Shugaba Mahmoud Abbas (dama) da kuma Firayim Minista Benjamin Netanyahu (hagu)
Image caption Shugaba Obama ya bayyana a bainar jama'a tare da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da kuma Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Shugaban Falasdinawa da Firayim Ministan Isra'ila sun jaddada kudurinsu na ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mahmoud Abbas da Benjamin Netanyahu sun bayyana hakan ne yayin da ake gab da shiga tattaunawa ta kai tsaye, wadda gwamnatin Obama ke shiga tsakani.

A ranar jajibirin tattaunawar a karo na farko cikin watanni ashirin, fadar gwamnatin Amurka ta White House ta cika da sautin kalaman da aka saba ji daga yankin na Gabas ta Tsakiya.

Firayim Minista Benjamin Netanyahu dai ya ce ya je wurin tattaunawar ne don samar da zaman lafiya ba don soki-burutsu ba.

Ya kuma ce Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas abokin tafiyarsa ne a yunkurin kawo zaman lafiya.

Shi kuwa Mista Abbas cewa ya yi za a iya cimma yarjejeniya a cikin shekara guda.

Ya kuma yi Allah-wadai da kisan wasu Isra'ilawa da 'yan bindiga suka yi a yankin Yammacin Kogin Jordan wanda Isra'ila ta mamaye.

Sai dai ya kara da cewa wajibi ne Isra'ilar ta amince da dakatar da gina matsugunan Yahudawa kwata-kwata.

A karshen wannan watan ne dai haramcin gina matsugunan da Isra'ila ta yi na wucin gadi zai zo karshe.

Abin da ba a tabbatar ba shi ne ko za a aiwatar da wadannan kalamai masu cike da kyakkayawan fata.

Karin bayani