Jam'iyyar ANPP na shirin zaben sabbin shugabanni

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Jamiyyar Adawa ta ANPP a Najeriya ta ce a ranar 6 ga wannan watan na Satumba, shugaban jam'iyyar Cif Edwin Ume Ezeoke da mukarrabansa, za su ajiye mukamansu.

Jamiyar ta ce wa'adin aikin shugabannin ya cika, kuma a ranar ne za su mika ragamar tafiyar da al'amuran jam'iyyar ga kwamitin rikon kwaryar da ta kafa.

ANPP ta kuma ce a ranakun 17 da 18 na Satumbar za ta gudunar da babban taron ta a birnin Abuja, domin zabar sabbin shugabannin jam'iyyar.

A makon da ya gabata ne wani bangare na ANPP ya yi shelar cewa ya sauke shugaban jam'iyyar da kuma mukarrabansa daga kan mukamansu.