EFCC ta karyata zargin yin kame kame

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta karyata jita-jitar cewa, wai za ta cafke wasu manyan jami'ai na ma'aikatun kudi da kananan hukumomi na wasu jihohin kasar, saboda suna adawa da takarar shugaba Goodluck Jonathan a zaben shekara mai zuwa.

EFCC ta mayar da martani ne ga wasu rahotannin da ke cewa, ofishin shugaban kasa ya ba ta umarnin ta kama wasu manyan jami'an gwamnati, a wasu jihohin kasar.

Wadannan jihohin sun hada da Kwara, Kebbi, Sokoto, Gombe da Jigawa.