Japan ta kakabawa Iran takunkumi

Firayim Ministan Japan, Naoto Kan
Image caption Firayim Ministan Japan, Naoto Kan

Majalisar ministocin Japan ta amince da karawa Iran takunkumi game da shirinta na nukiliya.

Matakan da Japan din ta dauka dai sun zarta wadanda Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanyawa Iran din, sun kuma haramta harka da wasu bankunan Iran da kuma hana zuba jari a bangarorin da suka shafi makamashi.

Babban sakataren majalisar ministocin Japan din, Yoshito Sengoku, ya ce daukar matakan ya zama wajibi don hana yaduwar makaman nukiliya.

“Ba wai gaban kanmu mu ka yi ba, mun dai yi kari ne a kan abin da Kwamitin Tsaro ya yi don tabbatar da hana yaduwar makaman nukiliya”, inji Mista Sengoku.