Tattaunawar Isra'ila da Falasdinawa

Shugaba Obama da shugabannin Isra'ila da Falasdinu
Image caption Shugaba Obama da shugabannin Isra'ila da Falasdinu

Shugabannin Isra'ila da na Falasdinawa sun tattauna kai tsaye a karo na farko a cikin kusan shekaru biyu a birnin Washington na kasar Amurka.

Jakadan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, George Mitchell, ya ce tattaunawar ta gamsar; bangarorin biyu kuma sun jaddada fatansu cewa tattaunawar za ta yi nasara.

Idan dai aka yi la'akari da tarihin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ba za a sa ran wannan karon za a tsinana wani abin a-zo-a-gani ba.

To amma Amurkawa sun nunawa bangarorin cewa lokaci na kurewa don haka ba zai yiwu a jinkirta fadawa juna gaskiya ba, al'amarin da shi ne zai kawo zaman lafiya a yankin.

Tattaunawar ta Washington dai ta haifar da sakamakon da ya gamsar da magoya bayanta ya kuma fusata masu adawa da ita.

A Isra'ila, masu ra'ayin rikau sun yi Allah-wadai da Benjamin Netanyahu, saboda cewa da ya yi Falasdinawa abokan tafiyarsa ne a yunkurin samar da zaman lafiya.

Hatta wasu jami'an gwamnatin hadin gwiwar da yake jagoranta sun ce tattaunawar ba za ta yi nasara ba domin kuwa Isra'ila ba za ta taba sassauta manufarta ta fadada matsugunan Yahudawa ba.

A bangaren Falasdinawa ma akwai mabambantan ra'ayoyi.

Yayinda wasu ke ganin an kara matsawa kusa da samun kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta, kungiyoyi irinsu Hamas sun yi suka a kan Mahmud Abbas saboda ‘ya mika wuya’ ga Isar'ila.

Nan da kusan makwanni biyu ne dai bangarorin za su sake ganawa ko da ya ke batutuwan da za su tattauna a kai ba su fito fili ba tukuna.

Karin bayani