An kafa majalisar kawo zaman lafiya a Afghanistan

Hamid Karzai, shugaban Afghanistan
Image caption Hamid Karzai, shugaban Afghanistan

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai, ya ce ya kafa majalisar kawo zaman lafiya ta kasa, domin cigaba da sasantawa da kungiyar Taliban, wadda kusan shekaru 9 kenan tana kokarin kawar da gwamnatin kasar.

Wata sanarwa daga ofishin mista Karzai din ta bayyana cewa, muhimmin mataki ne aka dauka, na tattaunawar kawo zaman lafiya.

An ce majalisar ta kunshi shugabannin jihadi, da masu fada-a-ji, da kuma mata. Nan gaba a cikin wannan watan ne za a bayyana sunayensu.

A watan Yunin da ya wuce ne, a lokacin wani taron da aka yi a birnin Kabul, aka amince a kirkiro wata majalisar koli ta zaman lafiya, domin soma tattaunawa tare da 'yan Taliban.