Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa

Taswirar Najeriya
Image caption Ministan ma'aikatar kudi ya ce tattalin arzikin kasar zai bunkasa

Ministan ma'aikatar kudi ta Najeriya, Mista Olusegun Aganga ya ce yanayin tattalin arzikin kasar zai bunkasa da kashi goma ko fiye da hakan cikin dari a karshen shekarar 2011 zuwa farkon shekarar 2012.

Mista Aganga ya shaidawa BBC cewa, masu zuba jari na son saka jari a kasar, kasancewa tattalin arzikinta, da ma na sauran kasashe masu tasowa ya bunkasa.

Ya ce: ''A duk mako masu son zuba jari daga kasashen duniya, biyu ko uku kan ziyarce ni.Su kan zo daga kasar Brazil,da Jamus, har da ma China, wadanda dukkaninsu ke son su zuba jari ne a Najeriyar.

Mista Aganga ya ce kasar ta fara wani shiri da zai samar da abubuwa more rayuwa,sa'annan gwamnati zata sayar da hukumar samar da wutar lantarki don inganta yanayin samun wutar.