Mutane 7 sun hallaka a harin da Amirka ta kai a Pakistan

Taswirar Pakistan
Image caption Taswirar Pakistan

Wani harin da Amirka ta kai ta sama, ya janyo hallakar akalla mutane 7, a yankin arewa maso yammacin Pakistan, kusa da iyaka da Afghanistan.

An harba makamai masu linzami ne akan wasu da ake jin 'yan gwagwarmaya ne, a wani gida da kuma a cikin wata mota, a wani kauye da ke arewacin Waziristan.

Jami'an gwamnatin Pakistan sun ce, daga cikin matattun har da wasu mayaka ukku, 'yan kasashen waje.

A wannan yankin ne wata kungiyar masu fafutukar Islama da ake kira Haqqani ta yi kaka-gida. Ana tsammanin ita ce ke da alhakin kai wasu manyan hare-hare akan dakarun kungiyar tsaron NATO a Afghanistan.