Zanga zangar adawa da korar 'yan kabilar Roma daga Faransa

Adawa da korar 'yan kabilar Roma daga Faransa
Image caption Adawa da korar 'yan kabilar Roma daga Faransa

Dubun dubatar masu zanga-zanga sun hallara a birnin Paris, domin kokawa da manufar gwamnatin Faransa, ta korar al'ummomin Roma daga kasar.

Masu zanga-zangar sun hallara a wani dandali, suna dauke da kwalaye inda aka yi rubuce-rubuce na zargin hukumomin Faransar da nuna wariyar al'umma.

Ana yin irin wannan zanga-zangar a wasu yankuna na kasar Faransar.

A watan da ya wuce, gwamnatin Faransar ta mayar da 'yan kabilar Romar su kimanin dubu guda zuwa kasashen Romania da Bulgaria.

Kasashen duniya sun soki wannan matakin da Faransar ta dauka. To amma bincike ya nuna cewa, fiye da rabin Faransawa na goyon bayan matakin.