Mutane sun mutu a Sudan

Shugaban kasar Sudan,Omar Al-Bashir
Image caption Mutane da dama sun mutu a Sudan

A kasar Sudan,'yan tawaye a yankin Darfur sun ce mutane da dama, wadanda akasarin su fararen hula ne, suka mutu sakamakon wani hari da sojoji suka kai.

Wani mai magana da yawun sojojin 'yan tawayen, ya zargi sojojin gwamnati da kai hare hare a wasu yankuna dake arewacin Darfur.

Rundunar hadin gwiwa ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta samu labarin wasu mutane dauke da bindigogi kan rakuma sun kai farmaki a wata kasuwa, inda suka yi ta harbin kan mai-uwa-da-wabi.

A nata bangaren, rundunar sojojin gwamnatin kasar, ta musanta cewa jami'anta ne suka kai harin.