Masu zanga-zanga sun jefi Tony Blair

Masu zanga-zanga a fusace sun rika jefa kwai, da kwalaben roba da kuma takalma, akan ayarin motocin tsohon Firaministan Birtaniya, Tony Blair, yayin da ya isa birnin Dublin, domin sa hannu a kan littafi na tarihin rayuwarsa, wanda aka kaddamar a wannan makon.

Wannan ne karon farko da Mista Blair din zai sa hannu a littafin a bainar jama'a.

Masu jifan dai basu sami tsohon Praministan ba.

To amma an rufe wasu shaguna a tsakiyar birnin, yayin da ake arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar.

Jami'an tsaron sun datse tituna da dama.

Su kuma masu zanga-zangar nuna adawa da yaki, sun rika yin wake-wake na zargin mista Blair da kaddamar da yakin da ya sabawa doka a Iraki.