'Malalar mai ta daina barazana ga muhalli'

Shugaban Amurka,Barack Obama(a hannun hagu),tare da Admiral Thad Allen
Image caption Admiral Thad Allen ya ce malalar man ba zata yi wata illa ga muhalli ba.

Wani jami'in Amurka dake kula da gyare gyaren da ake yiwa rijiyar mai ta kamfanin BP, da tayi ta zubar da mai a tekun Mexico, ya ce malalar bata da wata barazana ga muhalli.

Admiral Thad Allen ya bayyana haka ne bayan da injiniyoyin kamfanin, suka sauya daya daga na'urorin dake bakin murafen rijiyar man, a saman teku.

Sunan na'urar da aka sanya a yanzu shi ne mai kandagarki.

Aikin da zata yi shi ne tsayar da duk wata barazana da ka iya tasowa,wacce zata sa wata rijiyar man ta fara malala.

Ana zaton gazawar da irin wannan yunkuri ya yi a watan Aprilun da ya gabata ne, ya yi sanadiyar fashewar rijiyar man.

A yanzu dai masu gwaji wadanda suka hada da jami'an leken asirin Amurka na FBI, na yin nazari kan na'urar data samu matsalar a baya.

Sai dai hakan ba ya nufin yunkurin na baya-bayan nan,na nuni da shawo kan matsalar.

Injiniyoyin na shirin sanya kankare daga wata rijiyar ko-ta-kwana don ci gaba da aikin.

Ana saran fara shirin a makon gobe.