ETA za ta dakatar da bude wuta

'Yan Kungiyar ETA
Image caption 'Yan Kungiyar ETA

Haramtacciyar kungiyar ETA, ta 'yan awaren yankin Basque na kasar Spain, ta yi shelar dakatar da bude wuta ta kashin kai, a gwagwarmayar da take da makamai, domin kwato 'yancin kan yankin na Basque daga Spain din.

A cikin wani sakon bidiyon da ta aikawa BBC, kungiyar ta yi bayyani a kan matakin:

Kungiyar ta ETA ta ce tana son ta cimma burinta, ta hanyar lumana. To amma ba a san ko zata daina buda wutar na dindindin ba.

ETA dai na cikin tsaka mai wuya.

An kama wasu manyan 'ya'yanta, sannan kuma jam'iyyun siyasa na yankin Basque na ta kira a gareta da ta daina tada zaune tsaye.