Ma'aikata na yajin aiki a Gombe

Tawirar Najeriya
Image caption Ma'aikatan lafiya na yajin aiki a jihar Gombe

A jihar Gombe dake arewacin Najeriya, ma'aikatan kiwon lafiya sun fara wani yajin aikin gama gari, a ranar asabar don neman karin albashi daga wajen gwamnatin jihar.

Ma'aikatan na neman gwamnatin ne ta aiwatar da wani tsarin albashi na musamman ga ma'aikatan kiwon lafiyar, kamar yadda aka amince da shi a matakin gwamnatin tarayya.

Sun kuma zargi gwamnatin jihar da jan kafa wajen amincewa da wannan tsari,inda suka ce takwarorinsu na wasu jihohin kasar sun cimma yarjejeniya da gwamnatocin jihohinsu, amma nasu al'amarin ya faskara.

A nata bagaren,gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan lafiya,dakta Muhammad Isa Umar, ta ce ba zata ce komai akan batun ba, sai ranar litinin.