An kaddamar da kamfen din zaben Guinea zagaye na biyu

Zabe a Guinea-Conakry
Image caption Zabe a Guinea-Conakry

A Guinea, an bude kamfen din zaben shugaban kasar zagaye na biyu, wanda za a yi nan da makonni biyu.

An gudanar da zagayen farko a cikin lumana, a watan Yunin da ya wuce.

Ana kallon zaben a matsayin na farko a tsarin demokradiyya, tun bayan da Guinean ta sami 'yancin kai a 1958.

To sai dai zarge-zargen tafka magudi da sauran kura-kurai bayan zagayen farkon, sun sa an sami jinkiri wajen gudanar da zagayen na biyu.

A ranar Juma'ar da ta wuce, 'yan takarar biyu - watau tsohon Praminista Cellou Dalein Diallo, da jagoran 'yan adawa Alpha Conde, sun yi alkawari a rubuce, cewa zasu gudanar da yakin zaben cikin kwanciyar hankali, kuma duk wani kalubale da zasu yi, zasu yi shi ne a kotu.