Kasashen Afirka na kokarin cimma Muradun Karni

Paul Kagame, shugaban Rwanda
Image caption Paul Kagame, shugaban Rwanda

Shugabannin Afirka na yin taro a birnin Kigali na Rwanda, inda suke tattaunawa akan cigaban da aka samu kawo yanzu, a kokarin cimma uradun wannan karni na Majalisar Dinkin Duniya.

Nan da shekaru biyar ne ake fatan kawo karshen talauci, da kuma kyautata lafiyar jama'a da kuma ilimi.

Wasu mahalarta taron sun ce, ana fuskantar manyan kalubale wajen cimma muradun a nahiyar Afirka, irinsu yake-yake, da kuma rashin mayar da hankalin wasu gwamnatoci.

Wani wakilin majalisar dinkin duniya a wajen taron na Kigali ya ce, ya kamata kasashen Afirkar su yi koyi da Rwanda, wadda ya ce ta kama hanyar cika Muradun Karnin.