'Jam'iyyar RSD Gaskiya ta yi shirin shiga zabe'

Wata mace na kada kuri'a wajen zabe a jamhuriyar Nijar
Image caption Jam'iyyar RSD Gaskiya ta ce ta yi shirin shiga zabe

A jamhuriyar Nijar, jam'iyyar RSD Gaskiya ta ce a shirye take ta shiga dukan zabubukan da gwamnatin mulkin sojan kasar za ta shirya, domin mayar da kasar kan tafarkin dimokaradiyya.

Shugaban jam'iyar, Alhaji Shehu Amadu ya tabbatar da haka a jiya asabar, yayin wata hira da manema labarai a Yamai.

Ya kuma karyata wata jita-jita dake cewa ya fice daga Nijar tsawon watanni da dama, don gujewa binciken da sojoji ke yiwa tsofaffin magabatan kasar.

Alhaji Shehu Amadu ya jaddada matsayin jam'iyarsa na ci gaba da kasancewa cikin gungun jam'iyun siyasa na AFDR masu mulkin da sojoji suka hambarar.