Richard Dannatt ya zargi Tony Blair da Gordon Brown kan Iraq

Blair da Brown
Image caption Blair da Brown

Shugaban rundunar sojan Birtaniya mai ritaya, Janar Sir Richard Dannatt, ya zargi tsofaffin Firaministocin kasar na jam'iyyar Labour - watau Tony Blair da Gordon Brown - da sanyaya gwiwar dakarun Birtaniya a Iraki da Afghanistan.

Janar Dannat na zargin Gordon Brown ne da kasa samarwa rundunonin soja isassun kudade.

Ya ce shi kuma Tony Blair, ba shi da karsashin tilastawa Gordon Brown - wanda a lokacin shi ke kula da kudaden da gwamnati ke kashewa - na ya samar da kudaden da ake bukata, domin gudanar da yake-yaken biyu.

Bayan yayi ritaya a bara, Janar Sir Richard Dannat ya zama mashawarcin jam'iyyar Conservative ta fuskar tsaro, na zuwa wani dan lokaci.