Sa'ad Hariri ya amsa yin kuskure kan zargin Syria da kashe mahaifinsa

Praministan Lebanon, Sa'ad Hariri ya ce ya yi kuskure da ya zargi Syria da kashe mahaifinsa, tsohon praministan Lebanon Rafik Hariri, sakamakon wani harin bam a 2005.

Mr Hariri ya ce zargin yana da nasaba da siyasa, an kuma yi hanzari wajen yin sa.

Ya ce akwai tarihi na 'yan uwantaka tsakanin Syria da Lebanon, don haka shaidun da aka bayar na karya sun yaudari binciken da kasashen duniya suka gudanar game da kisan mahaifin nasa.

A wurare da dama an zargi Syria da kai harin, yayinda ita kuma ta yi ta musanta hannu a kin nasa.