An rantsar da Paul Kagame a Rwanda

An rantsar da Shugaba Paul Kagame na Rwanda a wa'adi na biyu na mulki.

A wajen wani buki a gaban dubban jama'a da kuma shugabannin Afrika fiye da 12 , Shugaban yayi alkawarin yin biyayya ga tsarin mulki da kuma tabbatar da zaman lafiya da lumana a kasar.