Labour ta samu kafa gwamnati a Australia

Jam'iyyar Labour mai mulki a Australiya ta sake samun nasara da karamar tazara, wanda ya kawo karshen kiki kakar siyasa da aka shiga ta fiye da makonni biyu.

Mace ta farko da aka zaba a matsayin Praministar kasar ta Australia Julia Gilliard ta ce a shirye take ta jagoranci tsayayyar gwamnati, bayanda 'yan independa guda biyu a majalisar dokokin kasar suka yanke shawarar mara ma ta baya.

Ms Gillard ta ce al'amarin da ya auku cikin makonni biyun da suka gabata ya tabbatar da cewa dimokradiyyar kasarsu na da matukar karfi sosai.