'Yan majalisu sun goyi bayan Gillard

Piraminstan Australia,Julia Gillard
Image caption 'Yan majalisu biyu sun marawa Gillard baya

A kasar Australia,'yan majalisu biyu cikin uku,wadanda basu da jam'iyyu, sun marawa Julia Gillard baya don kasancewa Piraministar kasar ta gaba.

Hakan zai bata damar kafa sabuwar gwamnati.

Dama dai 'yan majalisar su uku ne kawai, ake gani zasu yi maganin wannan dogon zango na siyasa da kasar ta samu kanta a ciki, sakamakon rashin samun wanda yai nasara mai rinjaye, a zaben da aka gudanar a watan jiya.

A majalisar kasar, jam'iyar adawa ta Conservative,wacce Tony Abbott ke jagoranta, nada kujeru 73.

Kana jam'iyar Labour, wacce ke da gwamnati nada kujeru 74, amma fa sai da ta samu goyon bayan jam'iyar Indipenda.