Madatsar ruwan Goronyo a jahar Sokoto ta fashe

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Daruruwan mutane sun tsere daga kauyukansu sun nufi saman tsaunukan dake kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar, sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu, bayan da wani bangare na madatsar ruwan Goronyo dake jahar Sakkwato ya fashe.

Wakilin BBC da ya ziyarci yankin ya ce ruwan ya mamaye kauyuka kusan 15, bayan faruwar lamarin a cikin daren jiya.

Ana kuma fargabar cewa, ruwan zai kara mamaye wasu garuruwan da ke kusa da kogin Rima, a jihohin Sakkwato da Kebbi.

Mako guda kenan dai tun lokacin da madatsar ruwan ta cika ta batse, kuma ruwan da ya malala ya shafe kauyen Kagara. Dubban jama'a sun koma gudun hijira.