Kona Kur'ani zai janyo matsala ga Amurka

Janar Petraeus, kwamandan dakarun NATO

Babban kwamandan dakarun kawance na NATO a Afghanistan, Janar David Petraeus, yayi gargadin cewa, mummunar martani ka iya biyo baya, muddin wata karamar mujami'ar evangelical a Florida, Amurka, ta aiwatar da shirinta na kona Al'Kur'ani, Mai tsarki, a ranar sha daya ga Satumba.

Cocin na Dove World Outreach Centre, ta kulla wannan shiri ne, domin dacewa da zagayowar shekara ta tara da aka kai hari kan New York da Washington, a Amurka.

Wakilin BBC ya ce daruruwan mutane sun yi zanga zanga game da shirin kona Al'kur'anin, a harabar masallacin dake Kabul babban birnin kasar, Afghanistan a jiya Litinin, inda suka kona tutar Amurka, tare kiraye- kiraye cikin fushi.

Sai dai a wata sanarwa da Pastor Jones, jagoran cocin ya fitar, ya ce ba zai fasa manufarsa ba.