Barazana ga rayuwar alkalan kotu a Najeriya

Harabar babban kotun daukaka kara
Image caption Harabar babban kotun daukaka kara a Abuja

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Anambra tana gudanar da bincike game da wani zargi da alkalan kotun sauraren kararrakin da suka shafi zaben gwamna da aka gudanar a jihar a farkon watan Fabrairun da ya gabata suka yi.

Alkalan kotun sun koka ne cewa, an aika musu da sakwanni ta wayar salula ana barazanar cutar da rayuwarsu walau ta hanyar sace su a yi garkuwa da su ko kuma a halaka

su.

Wannan lamari dai tuni ya sa alkalan kotun suka yanke shawarar ba za su iya ci gaba da gudanar da aikinsu ba. Mista Emeka Chukwu Emeka, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Anambra, ya shaida wa wakilin BBC ta wayar tarho cewa, rundunarsu ta sami koken da alkalan kotun sauraren kararrakin zaben suka yi cewa, wasu mutane da ba a kai ga tantance ko su wane ne ba, sun aika masu da wasu miyagun sakwanni ta wayoyin salula.

Za a tsananta bincike

"Zargin ya nuna an aika wa alkalan sakwanni ana yi musu barazana cewa, muddin basu bi wani mataki a hukunce-hukuncen da za su yanke a kan wasu karraki da aka kai musu ba, to fa za su gamu da gamonsu." In ji Mista Emeka

Mista Emeka Chukwu Emeka ya ce sun tuntubi wasu kamfanonin wayar salula, don su taimaka musu game da wannan bincike: "Muna so ne mu gano wa ya aika da wadannan sakwanni, kuma ta wanne kamanni, gami da mai yiwuwa wajen da aka aike da sakwannin."

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Anambran, ya shaida wa wakilin BBC cewar, babu takamaiman lokaci kammala binciken; "Bayanin da za mu samu daga kamfanonin wayar salular da muka tuntuba shi zai taka muhimmiyar rawa ga azamar binciken namu."

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce, sun tanadi tsauraran matakan tsaro ga alkalan kotun sauraren kararrakin zaben a masaukinsu da kuma inda kotun ke zama, amma kuma duk da haka alkalan sun yanke shawarar dakatar da zaman kotun.

Da ma dai wasu 'yan siyasa da suka gabatar da kara a gaban kotun sun zargi alkalan da nuna son rai a wasu hukunce-hukunce da suka yanke a ba da dadewa ba. Zargin da su kuma alkalan suka musanta.