Hukumar zaben Najeriya ta fidda jaddawalin zaben 2011

Parfesa Attahiru Jega, shugaban INEC
Image caption Parfesa Attahiru Jega, shugaban INEC

A Najeriya, hukumar zaben kasar mai zaman kanta, INEC, ta fitar da jaddawalin babban zaben da za a yi a kasar a shekara mai zuwa.

Jaddawalin ya nuna cewar za a fara ne da zaben 'yan majalisun tarayya - watau majalisar wakilai da ta dattijai - a ranar 15 ga watan Janairun badi, sannan kuma mako daya bayan haka, a ranar 22 ga watan na Janairun, za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Bayan haka akwai zaben gwamnonin jihohi da na majalisun jihohin, wanda za a yi a ranar 29 ga watan Janairun.

Har ila yau, jaddawalin na INEC ya nuna cewar, daga ranar 1 zuwa 14 ga watan Nuwamba mai zuwa, za a gudanar da rajisatar masu kada kuri'a, sannan a wallafa rajistar a ranar 16 ga watan Disamba.

Bugu da kari, daga ranar 11 ga watan Satumban nan, zuwa 30 ga watan Oktoba mai kamawa, an baiwa jam'iyyun siyasa damar gudanar da zaben fidda 'yan takararsu.

An kuma amince wa jam'iyyun siyasa su fara yakin neman zabe a bainar jama'a, daga ranar 17 ga watan Oktoba mai zuwa.