'Yara miliyan hudu sun mutu'

Kananan yara 'yan Afirka
Image caption Kungiyar Save the Children ta ce yara miliyan hudu sun mutu

Wani sabon rahoto da kungiyar agajin nan ta Save the Children ta wallafa ya ce yara miliyan hudu ne suka mutu a kasashe masu tasowa, sakamakon cututtukan da za a iya kaucewa.

Kungiyar ta dora alhakin hakan ne a kan sakacin da gwamnatoci ke nunawa ta fuskar kula da lafiyar kananan yaran.

Ta ce idan irin wadannan gwamnatoci basu tashi tsaye ba, abu ne mai wuya a cimma burin nan da ake da shi na rage yawan macemacen kananan yara na muradin karni a irin wadannan kasashe .

Wallafa rohoton ya zo ne makonni kafin wani babban taron kasashen duniya a kan cimma muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya.