'Yan adawa a Najeriya sun soki jadawalin zabe

Shugaban Hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Image caption Wasu 'yan adawa a Najeriya sun soki jadawalin babban zaben kasar

Wasu 'yan adawa a Najeriya sun soki jadawalin babban zaben kasar da hukumar zaben Najeriyar mai zanta ta fitar.

Alhaji Buba Galadima na jamiyyar adawa ta CPC ya shaida wa BBC cewar kamata yayi a gudanar da zabubbukan a rana guda sabanin lokaci zuwa lokaci da jadawalin INEC din ya tanadar.

Ya kara da cewar yin zaben a rana guda zai kauda duk wata almundaha ta zabe da ka iya faruwa

Hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato INEC dai ta fitar da jaddawalin babban zaben da za a yi a kasar a shekara mai zuwa a jiya.

Jaddawalin ya nuna cewar za a fara ne da zaben 'yan majalisun tarayya - watau majalisar wakilai da ta dattijai - a ranar 15 ga watan Janairun badi, sannan kuma mako daya bayan haka, a ranar 22 ga watan na Janairun, za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Bayan haka akwai zaben gwamnonin jihohi da na majalisun jihohin, wanda za a yi a ranar 29 ga watan Janairun.

Har ila yau, jaddawalin na INEC ya nuna cewar, daga ranar 1 zuwa 14 ga watan Nuwamba mai zuwa, za a gudanar da rajisatar masu kada kuri'a, sannan a wallafa rajistar a ranar 16 ga watan Disamba.

Bugu da kari, daga ranar 11 ga watan Satumban nan, zuwa 30 ga watan Oktoba mai kamawa, an baiwa jam'iyyun siyasa damar gudanar da zaben fidda 'yan takararsu.

An kuma amince wa jam'iyyun siyasa su fara yakin neman zabe a bainar jama'a, daga ranar 17 ga watan Oktoba mai zuwa.