Mutane dubu 8 na zaman gudun hijira a Goronyo

Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya
Image caption Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya

Hukumomin bayarda agaji a Najeriya sun ce, sun samu sauko da dubban mazauna kauyukan da suka tsere daga gidajensu, domin neman tsira daga ambaliyar ruwa a madatsar ruwa ta Gwaranyo, a jahar Sakkwato.

Kimanin kauyuka goma sha biyar ne hukumomin jahar suka ce sun tashi, bayan fashewar wani sashe na madatsar ruwan shekaran jiya da dare.

Yanzu haka dai mutane kimanin dubu takwas ne aka tsugunnar a wani sansani daf da iyaka da jamhuriyar Nijar.