An nada sabbin shugabannin rundinonin tsaro a Nijeriya

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sauke shugabannin rundunonin tsaron kasar da suka hada da na 'yan sanda, da sojan kasa, da na sojan sama da kuma na ruwa.

Shima shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, wato SSS an sauke shi daga kan mukaminsa.

Wannan mataki na ba zata dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun kalubalen tsaro a wasu jihohin arewacin Najeriya da suka hada da Borno da Bauchi.

Koda a watan Maris dai shugaban Najeriyar ya sauke babban mai bashi shawara ta fuskar tsaro bayan mummunan tashin hankalin da ya auku a jihar Pilato.