Hukumar gaskiya da sasanta al'uma ta Kenya na aikin warware rashin adalcin baya

A Kenya, hukumar binciken gaskiya da sasanta tsakanin al'umma ta kasar ta kaddamar da wani aikin samun hanyoyin tunkarar matsalolin da aka samu na cin zarafin bil'adama, bayan zaben kasar na 2008 da ya janyo takaddama.

Hukumar ta ce zata karbi bayanai daga shaidu, tare da duba abubuwa da suka faru tun daga 1963, lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Birtaniya.

Shugaban hukumar, Bethuel Kiplagat, ya ce zata gudanar da zama na sauraren jin bahasi daga jama'a, kuma a shirye suke su gurfanar da wasu a gaban kotu game da wasu laifukkan da aka aikata.

Wani wakilin BBC ya ce, hukumar ta dauri aniyar magance rashin adalcin da ba a warware ba -- wanda shi ne musababbin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben.