An yi gargadin game da barazanar kona Al-Qura'ani mai tsarki

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Barazanar da wani limamin Kirista na wata karamar coci a jihar Florida ta Amurka, ya yi na kona wasu kwafe kwafe na Kur'ani masu tsarki a ranar zagayowar hare haren sha daya ga watan Satumba, sun sa hukumar 'yan sanda ta duniya da kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurka gargadin yiwuwar barkewar mummunar tarzoma a wasu kasashe.

Hukumar Interpol ta ce akwai yuwuwar kai hari kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, matukar aka kona Al'Kur'anin mai tsarki.

Hakan nan ita ma ma'aikatar harkokin waje Amurka ta yi gargadi ga Amurkawa dake zaune a kasashen waje cewar akwai yuwuwar zanga zangar nuna kin jinin Amurka.

Tun farko dai Shugaba Obama ya yi wani roko na gaggawa ga wani limamin Kirista a Florida, wanda ke shirin kona Al'Kur'ani mai tsarki, da ya dakatar da wannan aniya tasa.

A cikin wata hirar talabijin da aka yi da shi, shugaba Obama ya ce yin hakan, daba ma ciki wuka ne, kuma hanya ce da zata kara baiwa 'yan kungiyar Alka'ida karin magoya baya.

Shugaba Obama ya ce, "idan yana saurare, ina fatan zai fahimci cewa abin da yake shirin yi, ga baki daya ya saba wa dabi'unmu na Amurkawa, wanda ke nuna cewar an gina wannan kasa ce kan harsashin bada 'yancin yin addini, da kuma hakuri da juna".

Hukumomin Amurka dai sun ce tsarin mulkin Amurka ya takaita masu iya matakan da zasu iya dauka kan batun.