Yantawayen LRA na haddasa cikas ga zaben raba gardama a Sudan

Rahotanni daga kudancin Sudan na cewa hare haren da kungiyar 'yan tawaye ta LRA ke kaiwa na janyo cikas ga shirye shiryen zaben raba gardamar da ake son gudanarwa cikin watan Janairu, game da ballewar yankin.

An bayyanawa wani taron mabiya adinin kirista cewa tun daga watan Mayu, an kashe mutane sama da dubu guda, an kuma sace wasu kwatankwacin wannan adadi.

Shugaban taron, bishop na Roman katolika na birnin Yambio Eduardo Hiboro Kussala ya ce mutane kimanin dubu dari da ashirin sun tsere daga gidajensu.

Lamarin dai ya haifar da matsaloli wajen sanar da jama'a game da zaben raba gardamar na Sudan.