Wasu sun yi sallar Idi yau a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewar wasu daga cikin musulman kasar sun ajiye azumi tare da gudanar da sallar idi a yau.

Hakan kuwa ta faru ne duk da sanarwar da shugabannin addinin musulunci na kasar suka bayar cewar ba a samu ganin wata ba a jiya.

Daga cikin wuraren da wasu suka gudanar da sallar har da birnin Sakkwato , inda wani malami addini mai ra'ayin sauyi ya jagoranci wasu dubban musulmin wajen gudanar da sallar.

Sai dai fadar mai alfarma Sarkin musulmi ta ce wannan sanarwar tana nan daram.

Da ma dai batun ganin watan Azumi da na Sallar a Najeriya ya jima yana janyo kace-nace tsakanin malaman addinin musulunci.