Sakamakon bincike kan lalata da yara a Cocin Belgium

Shugaban Cocin Belgium, Archibishop Andre-Joseph Leonard
Image caption Shugaban Cocin Belgium, Archibishop Andre-Joseph Leonard

Wani binciken gwamnati a Belgium ya karkare cewar lalatar da jami'an Cocin Roman Katolika suka yi da kananan yara ta faru kusan a kowane reshe na Cocin, kuma a cikin shekaru aru aru.

Hukumar ta ce mutane goma sha uku da lamarin ya rutsa da su tuni sun kashe kansu, sannan shidda sun yi kokarin yin haka.

Hukumar, wadda ta saurari shaidu daga kusan wadanda abun ya rutsa da su kusan dari biyar ta ce ta kadu daga irin shaidun, wadanda suka hada da bayanan fyade da lalata ta hanyoyi daban daban.

Galibin wadanda abun ya shafa dai yara ne maza, to amma an yi lalata da yan mata ma su fiye da 100 ma.

Sai dai an wanke Cocin daga tsararriyar rufa rufa.